Kungiyar Arewa ta marawa Saraki baya, ta caccaki Tinubu da kungiyar Buhari

Kungiyar Arewa ta marawa Saraki baya, ta caccaki Tinubu da kungiyar Buhari

Wata kungiya mai suna Arewa Youth for Peace and Security (AYPS), ta yabi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki akan shugabancinsa a majalisar dokokin kasar, wanda tace ya nuna misalan rabewar iko tare da inganta damokradiyya a kasar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Salisu Magaji, ya bayyana yabon ne jiya (Lahadi) a Bauchi yayin da yake bayyana ra’ayinsa akan jawabin da jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu yayi, cewa shugabancin Bukola Saraki ta kasance mai gaba da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Har ila yau, Magaji yayi Allah wadai akan jawabin da kungiyar labaran Buhari ta gabatar wanda shugaban ta Niyi Akinsiju da sakatarenta Cassidy Madueke suka sa hannu, wanda ke goyon bayan jawabin Tinubu.

Kungiyar Arewa ta marawa Saraki baya, ta caccaki Tinubu da kungiyar Buhari

Kungiyar Arewa ta marawa Saraki baya, ta caccaki Tinubu da kungiyar Buhari
Source: UGC

Kungiyar dake goyon bayan Buhari ta bayyana cewa kin amincewa da Saraki da mutanen jihar Kwara suka yi a zaben kasa na 2019 ya kasance sakamakon gaba da gwamnatin shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rashin hallaran alkali ya tsayar da gurfanar da zababben gwamnan Bauchi

Kungiyar ta bayyana cewa ba kamar wadanda suka gabata ba, David Mark, wanda ya kasance da kyakkyawar dangantaka tare da marigayi shugaban kasa Umaru Yar Adua kuma mutanen Benue sun sake zaban shi, Saraki bai yi nasaran ba “saboda son kai daya nuna ma kasar.”

Har ila yau, kungiyar ta bayyana Saraki a matsayin dan siyasa mara goyon baya na asali kuma mara iko a jihar Kwara.

Sai dai, Magaji wanda yayi magana a taron manema labarai a Bauchi a karshen makon da ya gabata, ya bayyana Allah wadai da kungiyar tayi akan Saraki a matsayin abu “mara amfani” inda ya kara da cewa Saraki ya kasance dan siyasa mai asali fiye da tsammani a siyasar Jihar Kwara wanda ya isa ya sa shi kishin kasa.

Magaji yayi nuni cewa babu kulle-kulle da kuma yakin neman kire-kiren karya akan ofishi ko martabar shugaban majalisa zai iya kauda martabar Saraki a tarihin Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel