Shuwagabannin APC sun nemi ya kyalesu da Yahaya Bello a zaben Kogi

Shuwagabannin APC sun nemi ya kyalesu da Yahaya Bello a zaben Kogi

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta jahar Kogi sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye goyon bayan da yake yi ma gwamnan jahar, Yahaya Bello yayin da zaben gwamnan ke karatowa a watan Nuwambar 2019.

Shugaban kungiyar masu ruwa da tsakin, Alex Kadiri ne ya mika wannan bukata ga shugaba Buhari, saboda a cewarsa Yahaya Bello bashi da kwarewar shugabanci ko ta miskala zarratan, kuma ya gaza biyan albashin ma’aikata da hakkokin yan fansho.

KU KARANTA: Yajin aikin Malaman Jami’a: Abin na damuna matuka – Inji Buhari

“Dama can jama’an Kogi ba su suka zabeshi ba, mutuwar Abubakar Audu ce tayi sanadiyyarsa zama gwamna, kuma gashi ya nuna ma kowa cewa bai iya shugabanci ba, ba zai iya kare hakkokin jama’an Kogi ba.

“Don haka muke kira a gareka daka janye goyon bayan da kake yi ma takarar Yahaya Bello a zaben gwamnan Kogi mai zuwa, idan kuma jam’iyyar ta tsayar dashi a matsayin dan takara, mun fadi zabe kenan.” Inji Alex.

Jiga jigan na APC sun bayyana cewa sun sha kai korafin Yahaya Bello ga uwar jam’iyyar APC a baya, wanda har ta kai APC ta kafa kwamitin bincike a karkashin Tony Momoh, sai dai yace har yanzu ba’a bayyana rahoton binciken ba.

“Haka zalika an sake kafa wani kwamiti na daban na Janar Garba, mun bayyana gaban kwamitin, kuma mun baje musu hujjoji da dama, amma har yanzu babu wanda ya bayyana rahoton binciken kwamitin.” Inji shi.

Sai dai kaakakin gwamnan jahar Kogi, Kingsley Fanwo ya musanta wannan zargi, inda yace a iya watanni 39 da Yahaya Bello yayi a matsayin gwamna, ya biya albashin watanni 38, sa’annan ya kara da cewa sun kammala gina hanyoyi a garin Ankpa, tare da kawo tsafa a aikin gwamnati, da sauran ababen cigaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel