PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya

PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da fadar Shugaban kasa sun yi musayar yawu kan ziyarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Birtaniya.

A shirin Politics today na Cannels Television, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, Mista Yemi Akinwonmi, yace ya kamata shugaban kasan ya rubuta ma Majalisa wasika akan manufarsa a kasar waje sannan ya mika mulki ga mataimakin shugaban kasa.

“Na san cewa bisa al’ada na fadin duniya, daidai ne cewa idan shugaban kasa zai tafi kasar waje, ko da manufar kansa ko na jama’a ne har na tsawon kwanaki bakwai, dole ya kasance ya aika rubutacciya ga majalisan don bayyana manufofinsa tare da mika mulki ga mataimakin shugaban kasa.

“Mutanen nan suna magana ne kamar Najeriya nasu ne, ba haka bane. Shugaban kasar na samun karfi ne daga al’umma. Kuma hakkin sa ne gaya wa yan Najeriya ba ga fadar shugaban kasa ba. Kudade kuma da zai kashe yayin tafiyan yana fitowa ne daga asusun kasa.”

PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya

PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya
Source: Facebook

Amman babban hadimin shugaban kasa, Mista Garba Shehu ya dage cewa shugaban kasar na iya gudanar da ayyukansa daga duk inda ya ga dama.

“Shugaban kasar bai yi kuskure ba da ya tafi kasar waje ba tare da sanar da majalisa ba a rubutaciyyar wasika. Kundin tsari tace kwanaki 21 ne kacal ta amince da shi. Wannan ne zai janyo a keta doka.

“Amman kamar yanda yake yanzu, babu dokar da aka keta, saboda haka, shugaban kasar na gudanar da ayyukansa daga duk inda yake.

"Daidai ne cewa shugaban kasan yana iya gudanar da ayyuka daga duk inda yake.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yawan mutanen Najeriya ya tasar ma miliyan 201

"Idan ka kasance sakatare na din-din-din kuma idan shugaban kasa ya kira ka daga kasar Abidjan ya baka umurnin gyara wata hanya, zaka fada mishi cewa shugaban kasa, kai ba dan Najeriya bane a Abidjan, baza ka yi aikin ba?"

Ya bayyana cewa “Kana tunanin cewa aikinka zai jira ka bayan hakan ya faru? Wannan lamarin mayar da hankali ne."

Wadannan bayanai suna zuwa ne kwana hudu bayan shugaban kasar ya tafi kasar waje wanda fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin tafiyar kansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel