Yanzu Yanzu: Rashin hallaran alkali ya tsayar da gurfanar da zababben gwamnan Bauchi

Yanzu Yanzu: Rashin hallaran alkali ya tsayar da gurfanar da zababben gwamnan Bauchi

Shirin da ake na gurfanar da zababben gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya hadu da cikas biyo bayan rashin hallaran alkalin da zai jagoranci shari’an.

An shirya gurfanar da Bala Mohammed wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), a yau Litinin, 29 ga watan Afrilu a gaban wata babbar kotun Abuja da ke Maitama kan tuhume-tuhume shida da suka hada da kaddamar da dukiyoyi na karya da kuma ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) bayanan karya.

Sai dai, yayinda Mohammed da lauyoyinsa suka isa kotu a ranar Litinin tare da lauyan EFCC, kotun bata zauna ba.

wani jami’in kotu ya bayyana wa majiyarmu ta Daily Trust cewa alkalin da zai jagoranci shari’an, Justis Yusuf Halilu na aiki kan korafin zabe a Abeoku,jihar Ogun.

Yanzu Yanzu: Rashin hallaran alkali ya tsayar da gurfanar da zababben gwamnan Bauchi

Yanzu Yanzu: Rashin hallaran alkali ya tsayar da gurfanar da zababben gwamnan Bauchi
Source: Twitter

Jami’in yace an sanya sabon rana domin gurfanarwar domin guje ma sake afkuwar abunda ya faru a yau inda bangarorin za su zo kotu sannan su tarar ba alkali a zaune.

KU KARANTA KUMA: EFCC na farautar Bala Mohammed ne saboda ya sha alwashin bincikar Gwamna Abubakar - Hadiminsa

A wajen kotun, lauyan EFCC, Wahab Shittu, yayinda yake jawabi ga manema labarai, ya karyata rade-radin cewa gurfanarwar farautar siyasa ce akan zababben gwamnan.

Yace kada wanda ya kalli abunda ke faruwa a matsayin wata barazana da EFCC ke yiwa wani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel