PDP ta zargi Buhari da hamdame N14trn cikin shekaru 4

PDP ta zargi Buhari da hamdame N14trn cikin shekaru 4

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa a kasar ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da sama da fadi akan kudade Naira tiriliyan 14 cikin shekaru hudu da ya yi akan mulki.

A cewar wata sanarwa daga sakataren labaran Jam’iyyar na kasa, Mista Kola Ologbondiyan ya yi zargin cewa, tsoron bankado badakalar satar tarin kudaden ne ya tilastawa Shugaban kasar neman tazarce na wasu shekaru hudu masu zuwa.

Sanarwar ta PDP ta ce kudaden da gwamnatin Buhari ta lakume sun hada da Naira Tiriliyan 9 daga Ma’aikatar man fetur din kasar kana da ma wasu triliyan 1 da biliyan dari 4 na tallafin man fetur da gwamnatin ta yi ikirarin cirewa sai kuma Naira Tiriliyan 1 da biliyan dari daya na danyen man fetur da gwamnatin ta sayarwa wasu kamfanoni marasa rijista ba kuma tare da ta sanya kudin a lalitar gwamnati ba.

PDP ta zargi Buhari da hamdame N14tr cikin shekaru 4

PDP ta zargi Buhari da hamdame N14tr cikin shekaru 4
Source: Twitter

Sanarwar PDP ta ci gaba da cewa akwai Naira biliyan 33 da aka wawure daga cikin kudin da aka warewa hukumar agaji ta NEMA kana wasu biliyan 18 wanda bangare ne na biliyan 48 da Majalisar zartaswa ta amince da warewa don kula da ‘yan gudun hijira a jihohin Borno Yobe da kuma Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Ku tabbatar Kiristoci sun zama shugabannin majalisa – Malamai ga yan majalisa

Har ila yau Ologbondiyan ya kuma yi ikirarin cewa adadin kudin da Najeriya ta ciwo bashi shi ne mafi muni a tarihi, inda yanzu haka ake bin gwamnatin Buharin bashi Naira tiriliyan 24 da biliyan dari 3 da tara.

A cewarsa cikin shekaru 3 gwamnatin Buhari mai ikirarin kawo sauyi a Najeriyar ta ranto kudin da yawansu ya kai tiriliyan 24 da rabi, ba kuma tare da wani gamsasshen aiki guda daya da talakawan kasar za su amfana ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel