Tiriliyan 14 aka yi gaba da su a Gwamnatin APC mai mulki inji Jam'iyyar PDP

Tiriliyan 14 aka yi gaba da su a Gwamnatin APC mai mulki inji Jam'iyyar PDP

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya watau PDP, tayi ikirarin cewa an sace kudi har fiye da Naira Tiriliyan 14 a gwamnatin APC ta shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin shekaru kusan 4 a kasar.

Jam’iyyar PDP ta bayyana wannan ne a Ranar Lahadi 28 ga Watan Afrilun nan inda take zargin gwamnatin Buhari da tsoron barin karagar mulki domin gudun a binciki irin barnar da ta tafka a cikin shekarun da tayi a mulki.

PDP tayi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakataren ta na yada labarai na kasa watau Kola Ologbondiyan. Ologbondiyan ya bayyanawa manema labarai wannan ne a Abuja, yana mai lissafo irin badakalar gwamnatin APC.

KU KARANTA: Atiku ya hango nasarar rushe zaben da aka yi a 2019

Ologbondiyan yace ana zargin Naira Tiriliyan 9 ya bace daga ma’aikatan man fetur kamar yadda hukumar NNPC ta fasa kwai kwanaki. Bayan nan kuma PDP tace an yi awon gaba da Tiriliyan 1.4 da sunan tallafin man fetur a kasar.

Jam’iyyar adawar tana kuma zargin gwamnatin APC da satar wasu Tiriliyan 1.1 na kudin man fetur da sunan wasu kamfanoni da ba ayi wa rajista ba. Kakakin jam’iyyar yace an kuma sace wasu Naira Biliyan 33 daga asusun hukumar NEMA.

KU KARANTA: Buhari ya sa ranar da zai sallami Ministocinsa daga aiki

Har wa yau, jam’iyyar hamayyar ta PDP tana zargin gwamnatin APC mai mulki da yin sama da fadi da kudi har Naira Biliyan 18 da majalisar tarayya ta ware domin dawainiyar masu gudun hijira a yankin Arewa maso Gabas a shekarar 2017.

Mista Ologbondiyan yake cewa ba a nan kurum barnar gwamnatin nan mai-ci ta tsaya ba, domin kuwa ta ci bashin sama da Naira Tiriliyan 12 da ba a san ayyukan da aka yi da su ba. APC dai ba ta maida martani kan wadannan zargi ba.

A cewar Kakakin na PDP, irin wannan barna da gwamnatin APC tayi, shiyasa tayi kokari wajen ganin an murde zaben 2019, sannan ta hana kotu tayi aikin karar zaben 2019, domin ta cigaba da mulki yadda za ta tserewa duk wani bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel