EFCC na farautar Bala Mohammed ne saboda ya sha alwashin bincikar Gwamna Abubakar - Hadiminsa

EFCC na farautar Bala Mohammed ne saboda ya sha alwashin bincikar Gwamna Abubakar - Hadiminsa

Zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammaed ya zargi gwamnan jihar mai ci, Mohammed Abubakar da gayyatan jami’an hukumar EFCC don bata mishi suna gabannin rantsarwa da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu.

Bala Mohammed zai bayyana a kotu a yau Litinin a kotu 26 dake Babban kotun Birnin Tarayya a Maitama a Abuja don fuskantan laifuffukan da suka shafi bayyana kaddarori na karya.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) tayi ikirarin cewa Mohammed ya gaza bayyana dukkan kaddarorinsa a bayyanarsa a kotu a baya. Hukumar EFCC a lamari mai kama da haka ta gabatar da laififfuka shida a cewar bayanai da aka gabatar.

EFCC na farautar Bala Mohammed ne saboda ya sha alwashin bincikar Gwamna Abubakar - Hadiminsa
EFCC na farautar Bala Mohammed ne saboda ya sha alwashin bincikar Gwamna Abubakar - Hadiminsa
Source: UGC

Ibrahim Danlami, hadimin zababben gwamnan, ya bayyana cewa Gwamna Abubakar wanda ya karbi sakamakon zabe a baya inda ya aika ma Bala Mohammed sakon murna sannan ya tafi kotu bayan zababben gwamnan ya sha alwashin bincikan ayyukan gwamnatin Abubakar ne ya shirya tuggun.

KU KARANTA KUMA: Ku tabbatar Kiristoci sun zama shugabannin majalisa – Malamai ga yan majalisa

A wani hira da Bala Mohammed kawanan nan, yace “kuma idan kakakin majalisan wakilai ya gano wassu takardu wadanda ke nuna cewa fiye da ma’aikatan bogi 2,000 ne aka saka sunayen su don cin albashin jihar Bauchi a shekaru hudu da suka gabata kuma akalla fiye da naira biliyan 400 ne ya shigo Bauchi kuma bamu ga aiki na naira biliyan 5 ba”.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel