Nadin Ministoci: APC da na hannun-daman Buhari za su sha mamaki

Nadin Ministoci: APC da na hannun-daman Buhari za su sha mamaki

Mun fara jin kishin-kishin daga Jaridar Vanguard cewa shugaba Muhammadu Buhari zai maida hankali ne wajen kwarewa da sanin aiki idan ya tashi zabo sababbin Ministocin da zai yi aiki da su a gwamnati.

Jaridar tace shugaba Buhari zai sabawa abin da aka saba yi a da na dauko Ministoci domin sakawa wadanda su kayi wa jam’iyya hidima a zabe. Wannan ya sa har na kusa da shugaban kasar su ka rasa inda ya sa gaba a wannan karo.

Ainihin abin da ya sa shugaba Buhari ya tattara a tafi Landan kwanan nan shi ne domin ya kauracewa manyan jam’iyyar APC da kuma wasu na-kusa da shi da wadanda ake jin maganar su a kasar, wajen zakulo Ministocin sa na 2019.

Majiyar ta ke cewa shugaban kasar zai so ya samu sariri yayi aikin zakulo da wadanda za su rike masa mukamai a gwamnatin sa da za ta zarce a watan gobe. Majiyar tace za ayi mamaki idan aka ji sunayen sababbin Ministoci na bana.

KU KARANTA: Atiku ya hango nasarar karbe mulki daga hannun Buhari

Nadin Ministoci: APC da na hannun-daman Buhari za su sha mamaki
Shugaba Buhari zai bada karfi wajen sanin aiki a zaben Ministoci
Source: Twitter

Shugaban kasar zai yi wa’adin sa na karshe ne don haka yake kokarin ganin ya nemo kwararrun da za su taimaka masa wajen tafiyar da kasar inji wannan Majiya mai karfi da ke ganin cewa har na kusa da Buhari za su ga abin mamaki.

Vanguard tace shugaban kasar ya san dole ya tashi tsaye wannan karo. Rahoton ya kuma bayyana cewa shugaba Buhari zai bi dokar kasa da tace dole a fito da akalla Minista guda daga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja.

A halin yanzu, wasu Ministoci ba su yi aikin da ya kamata ba, yayin da wasu ke ta faman fada a tsakaninsu. Shugaban kasar duk ya san da wannan matsaloli kuma zai yi kokarin gyara wasu a wannan wa’adin na sa na biyu da zai yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel