‘Yan takarar APC sun lashe zaben kananan hukumomi a Zamfara

‘Yan takarar APC sun lashe zaben kananan hukumomi a Zamfara

Mun samu labari cewa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ce ta lashe kaf zaben kananan hukumomin da aka yi a Jihar Zamfara. Hukumar zabe na jihar Zamfara ta bayyana mana wannan.

Hukumar zabe mai zaman kan-ta na jihar Zamfara ta sanar da cewa ‘yan takarar APC sun lashe zaben da aka yi a kananan hukumomin jihar a karshen makon jiya. Jam’iyyu 42 ne su ka shiga cikin wannan zabe aka gwabza da su.

Kamar yadda mu ka samu labari daga hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, Shugaban hukumar zabe na jihar Zamfara, Alhaji Garba Muhammad ya sanar da cewa APC tayi nasara a duka kananan hukumomin da ake da su.

Haka zalika shugaban hukumar ZSIEC ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta lashe kujerun Kansiloli 147 na jihar Zamfara. Jam’iyyar ta APC ta samu shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu 28 inji Alhaji Garba Muhammad.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta sake lashe wani zabe da aka yi a Legas

Idan ba ku manta ba, a cikin ‘yan kwanakin nan ne jam’iyyar PDP mai hamayya da kuma Accord Party su ka sheka kotu inda su ka nemi a dakatar da gudanar da zaben jihar da sunan cewa ba a sanar da su game da shirin zabe ba.

Ga sunayen sababbin shugabannin kananan hukumomin nan da kuma yawan kuri’un da su ka samu a zaben na Ranar 27 ga Watan Afrilun nankamar yadda NAN ta rahoto.

1. Anka – Ahmad Balarabe with 38,698

2. Birnin/Magaji – Muhammad Umar – 67,002

3. Bungudu – Abdul’aziz Ahmad – 75,219

4. Bakura – Dandare Dandako – 65,060

5. Bukkuyum – Nasiru Zarumi – 64,049

6. Gummi – Kabiru S-Aski – 53,668

7. Gusau – Alhaji Babangida – 115,142

8. Kaura/Namoda – Lawal Abdullahi – 62,051 .

9. Maradun – Ahmad Abubakar – 50,812

10. Maru – Salisu Isah – 75,274

11. Shinkafi – Sani Galadi – 48,469

12. Talata-Mafara – Lawal Marafa – 70,625

13. Tsafe – Aminu Mudi – 74,521

14. Zurmi – Awwal Bawa – 76,510

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel