Ba talauci bane ya sa ni shiga filin tono ma’adinai ba, neman halal nake – Isa Yuguda

Ba talauci bane ya sa ni shiga filin tono ma’adinai ba, neman halal nake – Isa Yuguda

Toshon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda yayi tsokaci, biyo bayan cece-kuce da ake tayi a kafafen sada zumunta sakamakon billar wani bidiyonsa da ya shahara, inda aka gano shi a filin tonon ma’adinai tare da leburorinsa, inda wasu ke ganin kamar talauci ce tayi masa kamun kazar kuku.

A wata zantawa da Muryar Amurka ta yi da tsohon Isa Yuguda, ya karyata batun cewa talauci ke cikinsa inda ya bayyana cewa har ya zuwa yanzu yana da rufin asirinsa, kuma ya fara aikin tonon ma’adanai ne domin ya nemi halal din sa.

Mallam Isa, ya bayyana cewa shi da kansa ya tura hoton bidiyon kafar sada zumunta, domin ya zaburar da matasa su mike domin neman na kansu, ganin cewa ya rike manyan mukamai a rayuwarsa hakan bai hana shi yin amfani da karfinsa wajen neman halal.

Ba talauci bane ya sa ni shiga filin tono ma’adinai, neman halal nake – Isa Yuguda
Ba talauci bane ya sa ni shiga filin tono ma’adinai, neman halal nake – Isa Yuguda
Source: Depositphotos

Yuguda dai ya yi ayyuka da suka hada da Ministan Sufuri da kuma Manajan Daraktan Bankunan Najeriya, kafin daga baya kuma ya zama gwamnan jihar Bauchi har na tsawon shekaru takwas.

KU KARANTA KUMA: Sai na kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Shugaban yan sanda ya dau alkawari

Bayan saukarsa daga kujerar gwamna, kamar yadda ya fadawa Muryar Amurka, ya koma gonarsa ne da gwamnatin tarayya ta bashi tun asali wadda ke dauke da ma’adanai, ya kuma ci gaba da aikin hako ma’adanai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel