Yajin aikin Malaman Jami’a: Abin na damuna matuka – Inji Buhari

Yajin aikin Malaman Jami’a: Abin na damuna matuka – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya ke yawan ajiye kayan aiki su shiga yajin aiki, inda ya bayyana cewa hakan na tayar masa hankali matuka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin bikin yaye daliban jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria, wanda ya gudana a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, inda ya samu wakilcin shugaban hukumar kula jami’o’in Najeriya, NUC, Farfesa Abubakr Adamu Rasheed.

KU KARANTA: Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna

Yajin aikin Malaman Jami’a: Abin na damuna matuka – Inji Buhari

Yajin aikin Malaman Jami’a: Abin na damuna matuka – Inji Buhari
Source: Getty Images

Buhari yace duk wani yajin aiki da kungiyar malamai suka gudanar yana gurgunta cigaban karatu, tare da gurgunta tsare tsaren jami’iar kanta, ya kara da cewa abin takaici ne idan aka dubi adadin lokacin da aka bata ma dalibai a dalilin yajin aiki.

Da wannan ne shugaba Buhari ya nemi kungiyoyin malaman jami’a da sauran kungiyoyin dake jami’a dasu kasance masu la’akari da bukatun wasu ba wai nasu kadai ba a duk lokacin da suke tunanin shiga yajin aiki.

Inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati na sane da duk wasu matsalolin da ake fuskanta a jami’o’i, kuma bakin gwargwado zasu yi iya kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalolin don cigaban ilimi, amma fay a tuna musu cewa hakan zai samu ne kadai idan an samu kwanciyar hankali a jami’o’in.

Haka zalika shugaban kasa ya jinjina ma jami’ar ABU ta yadda take fadada ayyukanta, kamar samar da tsarin samun ilimi daga nesa, hadin gwiwa da kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi daban daban, inda yace hakan ya taimaka wajen sama ma dalibai da dama guraben karatu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel