Masu damfarar mutane a Kasar Amurka daga Najeriya sun fada hannun hukuma

Masu damfarar mutane a Kasar Amurka daga Najeriya sun fada hannun hukuma

Mun samu labari cewa Mutanen Najeriya 9 aka kama a cikin kasar Amurka da laifin damfarar Bayin Allah da dama inda su ka tara kudi har fam Dala miliyan 3.5 a sanadiyyar wannan danyen aiki.

Babban Alkalin shiyyar Kudancin Birnin New York, Geoffrey S. Berman, da kuma wani babban jami’in da ke bincike a Yankin Florida da kewaye a cikin Amurka, James C. Spero, su ka bayyana cafke wadannan mutanen Najeriya da ke ta'adi.

Jami’an kasar Amurkan sun sanar da Duniya wannan ne a Ranar Alhamis, 25 ga Watan Afrilu. Wadannan ‘Yan Najeriya da aka kama, su na yaudarar jama’a ne ta hanyar soyayya da kuma harkar kasuwancin man fetur na karya.

James C. Spero ya bayyana sunan wadannan mutane da aka kama a matsayin; Oluwaseun Adelekan (wanda aka fi sani da Sean Adelekan), da Olalekan Daramola, Solomon Aburekhanlen, da kuma wani mai suna Gbenga Oyeneyin.

KU KARANTA: EFCC za ta kai Kotu Gwamna mai-jiran mulki Kotu da laifin cin rashawa

Har wa yau, sauran wadanda hukumar kasar Amurkan ta cafke sun hada da; Abiola Olajumoke, Temitope Omotayo, Bryan Eadie, Albert Lucas da kuma wani Ademola Adebogun, wanda shi ma ‘Dan Najeriya kamar duk sauran.

Kowane daga cikin wadannan mutane da aka kama na iya fuskantar daurin shekaru 20 a gidan yari idan laifin na sa yayi tsanani. Ba wannan ne karon farko da aka kama ‘Yan Najeriya su na irin wannan mugun barna a kasar waje ba.

Babban Mai shari’a na kasar Amurkan Geoffrey S. Berman, yace wadannan mutane na damfarar Bayin Allah ne ta hanyar aika masu sakonnin e-mail na yanar gizo. Wadanda ake zargin kuma su kan sakaya asalin sunayen su inji Berman.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel