Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna

Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wani mutumi mai suna Abubakar Ibrahim mai shekaru 37 wanda take tuhumar da zargin kashe babban basaraken jahar Kaduna, Agwam Adara, Maiwada Galadima bayan yayi garkuwa dashi.

Legit.ng ta ruwaito a watan Oktobar bara ne yan bindiga suka yi awon gaba da Galadima da nufin yin garkuwa dashi har sai an biyasu kudin fansa, inda daga bisani kuma suka kasheshi duk kuwa da cewa an biyasu kudin fansa.

KU KARANTA: Likitoci sun bankado dimbin matsaloli dake tattare da lafiyar Zakzaky

Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna
Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna
Source: Facebook

Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Frank Mba ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu, inda yace sun kama Salisu ne a ranar 15 ga watan Afrilu a garin Rigachikun dake cikin karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna.

Sanarwar ta kara da cewa Salisu da kansa ya amsa aikata laifin yin garkuwa da Galadima, tare da halakashi, bugu da kari ya bayyana yadda shi da wasu abokan aikinsa suke satar mutane da yin garkuwa dasu a Kaduna.

Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna
Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna
Source: Facebook

Haka zalika kaakakin yace Yansanda sun samu nasarar kama wasu gungun barayin mutane su goma sha takwas bayan sun kama shugabansu, kuma babban malamin tsubbun dake basu sa’a mai suna Salisu Abubakar.

Yansanda na musamman dake gudanar da aiki na musammanmai taken Operation Puff Adder, daya kunshi jami’an IRT da TIU ne suka jagoranci wannan aiki daya kai ga kama masu garkuwa da mutanen da suka fitinin al’ummar Kaduna.

Yansandan sun yi sa’ar bankado sansanonin barayin daban daban da suka hada da Birnin Gwari Rijana, Katari, Mai Daro, da kuma Dajin Buruku, duk a cikin jahar Kaduna, sa’annan sun kakkamo barayin ne daga sassa daban daban na jahohin Kaduna, Katsina, Neja da Kogi, inda suke fakewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel