Hare haren Bom: Gwamnati ta haramta ma matan Musulmai sanya nikabi

Hare haren Bom: Gwamnati ta haramta ma matan Musulmai sanya nikabi

Gwamnatin kasar Sri Lanka ta sanar da haramta ma Mata Musulmai sanya kowanne irin nikabi a bainar jama’a, inda gwamnatin tace ta dauki wannan mataki ne biyo bayan haren haren ta’addancin da aka kai a kasar a ranar bikin Easter.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin kasar ce ya fitar da wannan sanarwar a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu, inda tace ta haramta sanya duk wani abu da zai hana jami’an tsaro gane mutumin daya sanya.

KU KARANTA: Likitoci sun bankado dimbin matsaloli dake tattare da lafiyar Zakzaky

Hare haren Bom: Gwamnati ta haramta ma matan Musulmai sanya nikabi

Hare haren Bom: Gwamnati ta haramta ma matan Musulmai sanya nikabi
Source: UGC

Sanarwar data fito daga fadar shugaban kasar Sri Lanka, Maithripala Sirisena ta bayyana cewa dokar zata fara aiki ne daga ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu a karkashin matakin dokar ta baci data dauka a binciken da take yi don kama dukkanin masu hannu cikin harin ta’addancin daya kashe sama da mutane 250.

Sai dai wata kungiyar shuwagabannin Musulman kasar sun yaba da wannan mataki da kasar Sri Lanka ta dauka, inda suka nemi Musulman kasar su yi biyayya ga dokar ta hanyar nisantar sanya duk wasu kaya da zasu hana a gane fuskokinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa yawancin wadanda suka mutu a harin ta’addancin yan kasar Sri Lanka ne, amma akwai mutane 40 yan kasashen waje da suka suka da kasar Birtaniya, Amurka, Australia, Turkey, India, China, Denmark, Netherland da Portugal.

A yanzu haka gwamnatin kasar ta kama sama da mutane 100 da take zargi da hannu cikin harin, daga cikinsu akwai yan kasashen Syria da Misar, wanda a yanzu haka suna can shan tambayoyi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel