Likitoci sun bankado dimbin matsaloli dake tattare da lafiyar Zakzaky

Likitoci sun bankado dimbin matsaloli dake tattare da lafiyar Zakzaky

Kwararrun likitoci da suka shigo da kasashen waje suka duba lafiyar shugaban kungiyar yan shia daya dade a hannun gwamnati, Malam Ibrahim Zakzaky sun bayyana cewa Zakzaky na cikin mawuyacin hali sakamakon gano wasu dimbin matsaloli a tare dashi da matarsa da suka yi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da wannan ne likitocin da suka fito daga kasar Iran suka bayyana bukatar a fitar dashi daga Najeriya domin ya samu ingantaccen kulawa a manyan Asibitocin duniya tare da matar tasa a kasar waje.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An sanar da ranar sakin sakamakon jarabawar JAMB

Guda daga cikin likitoci mai suna Kazim Akber Dhalla, wanda kwararren likitan ido ne ya bayyana cewa “Duba da binciken lafiyarsa da muka yi, daga shi har matarsa suna tattara da matsaloli da dayawa, wasu mun ganosu anan Najeriya, wasu kuma muna ganin har sai an kaisu manyan Asibitoci a kasashe waje don samun kulawa.”

A makon daya gabata ne gwamnatin Najeriya ta baiwa likitocin damar shigowa Najeriya domin su duba lafiyar Zakzaky, wanda hakan tasa ofishin jakadancin Iran dake Najeriya ta fidda sanarwar godiya ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bisa amincewar da yayi.

Kaakakin ofishin jakadancin na Iran, Syede Mousavi ne ya fidda wannan sanarwa, inda yayi fatan wanan dama zata baiwa gwamnatin Najeriya daman tattaunawa da kungiyar yan shia ta Najeriya, tare da sakin babban malaminta dake daure.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel