Yansanda sun cafke gagararrun masu garkuwa da mutane 18 a Kaduna (Hotuna)

Yansanda sun cafke gagararrun masu garkuwa da mutane 18 a Kaduna (Hotuna)

Rundunar Yansandan Najeriya na musamman sun samu wata gagarumar nasara yayin da suka kama gungun wasu gagga gaggan barayin mutane su goma sha takwas, bayan sun kama malamin tsubbunsu dake basu sa’a mai suna Malam Salisu Abubakar.

Legit.ng ta ruwaito Yansanda na musamman dake gudanar da aiki na musammanmai taken Operation Puff Adder, daya kunshi jami’an IRT da TIU ne suka jagoranci wannan aiki daya kai ga kama masu garkuwa da mutanen da suka fitinin al’ummar Kaduna.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An sanar da ranar sakin sakamakon jarabawar JAMB

Yansanda sun cafke gagararrun masu garkuwa da mutane 18 a Kaduna (Hotuna)

Yansanda sun cafke gagararrun masu garkuwa da mutane 18 a Kaduna
Source: Facebook

Yansandan sun yi sa’ar bankado sansanonin barayin daban daban da suka hada da Birnin Gwari Rijana, Katari, Mai Daro, da kuma Dajin Buruku, duk a cikin jahar Kaduna, sa’annan sun kakkamo barayin ne daga sassa daban daban na jahohin Kaduna, Katsina, Neja da Kogi, inda suke fakewa.

Sanarwa daga bakin kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Frank Mba ta bayyana sunayen barayin kamar haka;

Abubakar Ibrahim Dan Habu (37)

Johnson Okafor (44)

Shaibu Iliyasu Smally (20)

Ishaik Dabo Keke (38)

Mohammed Nasiru (25)

Aminu Haruna (25)

Shafiu Alhaji Gudau (25)

Auwalu Hamisu (24)

Ado Ya'u (35)

Ibrahim Yusuf (30)

Ibrahim Audu (22)

Salisu Ajah (50)

Nasiru Umaru (25)

Magaji Abubakar (27)

Salisu Ali (18)

Lawal Shadari (22)

Junaidu Lawal (18)

Usman Musa (43)

Daga karshe kaakaki Mista Mba yace sun kwato makamai da suka hada da bindigar AK-47 guda 22, kananan bindigu 5, da kuma alburusai da dama.

A wani labarin kuma rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama mutumin daya jagoranci yin garkuwa da wani babban basaraken jahar Kaduna, Agwan Adara, tare da halakashi bayan ya amshi kudin fansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel