2019: Atiku ya fadawa Magoya-bayansa cewa zai karbe mulki daga hannun Buhari

2019: Atiku ya fadawa Magoya-bayansa cewa zai karbe mulki daga hannun Buhari

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake tadowa magoya bayansa kwarin gwiwar cewa zai karbi mulkin kasar nan a hannun APC a kotu.

Atiku Abubakar ya jaddada cewa zai samu nasara a shari’ar da yake fama a kan zaben shugaban kasa da ake yi tsakanin sa da shugaba Muhammadu Buhari. Atiku yake fadawa Magoya bayansa cewa akwai alamun nasara a kotu.

Kamar yadda labari ya zo mana, Mai taimakawa Atiku Abubakar da shawara a kan harkokin Matasa, Ambasada Aliyu Bin Abbas, ya fitar da jawabi a karshen makon nan inda ya nemi Magoya bayansa su fara sa ran ganin nasara.

KU KARANTA: Lauyoyin Atiku su na kuka da taurin kan Hukumar INEC

A jawabin na Atiku Abubakar wanda ya aikawa Magoya bayansa har su miliyan 18 a Najeriya mai suna: “A MESSAGE OF HOPE TO THE OVER 18 MILLION ATIKULATED FAMILY MEMBERS”, ya bayyana cewa zai karbe mulkin Najeriya.

‘Dan takarar na PDP a zaben 2019 yake cewa ba a taba shiga kotun sauraron karar zabe da tarin hujjoji kamar a ture, kamar irin zaben bana ba. Atiku Abubakar ya kara da cewa jam’iyyar PDP ta dauko hanyar karbe nasarar zaben 2019.

KU KARANTA: PDP tana so a karbe nasarar da APC ta samu a zaben kano

Alhaji Atiku ya yabawa irin jajircewa da tsaya tsayin-dakan da Magoya bayansa su kayi wajen ganin sun zabe PDP duk da irin kalubalen da aka samu na dage zaben kasar. Atiku yace wasu ‘yan kasar ba su taba kada kuri’a ba, sai a kan sa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda yayi takara da shugaban kasa Buhari a bana, ya bayyana yadda wasu masu goyon bayansa su ka rika biyan kudi daga aljihunsu domin a basu katin zabe don kurum su zabi am'iyyar PDP.

Atiku yake fadawa jama’an sa cewa sam ka da su karaya domin a karshen tikewa, PDP za ta samu nasara a shari’ar da ake yi a kotu, inda zai karbi mulkin kasar domin ya samawa jama’a aikin yi, sannan kuma Najeriya ta hau kan saiti.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel