Jam'iyyar APC ta samu galaba a kan PDP a zaben kujerar Ajeromi/Ifelodun

Jam'iyyar APC ta samu galaba a kan PDP a zaben kujerar Ajeromi/Ifelodun

- Jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben Majalisa da aka yi a Legas

- ‘Dan takarar APC ya samu galaba a kan PDP a Ajeromi da Ifelodun

Mun samu labari cewa jam’iyyar APC mai mulki tayi nasara a zaben majalisar wakilan tarayyar da aka yi a jihar Legas. A Ranar Asabar 27 ga Watan Afrilun nan ne aka sanar da sakamakon zaben na cikin karshen makon nan.

Kamar yadda labari ya zo mana, an yi zaben ne cikin tsananin tsaro, inda ‘dan takarar jam’iyyar APC yayi galaba a kan jam’iyyar adawa ta PDP. Kolawole Taiwo, ya lashe zaben majalisar tarayya na mazabar Ajeromi da Ifelodun.

KU KARANTA: Ban yi nadamar tserewa daga PDP in dawo APC ba - Akpabio

Jam'iyyar APC ta samu galaba a kan PDP a zaben kujerar Ajeromi/Ifelodun

Wasu daga cikin taron Magoya bayan Jam'iyyar APC a Jihar Legas
Source: UGC

Hukumar INEC mai zaman kan-ta, ta sanar da cewa Kolawole Taiwo ya doke Rita Orji ta jam’iyyar PDP mai hamayya da karamar tazara. APC ta samu kuri’a 36,115 a zaben, yayin da ‘yar takarar PDP kuma ya samu kuri'a 32, 557.

Farfesa Mathew Ilorin a jami’ar Legas, wanda yayi aiki a matsayin Malamin zabe na INEC, shi ya sanar da wannan sakamako. An shirya wannan zabe ne domin karasa tattara kuri’un akwatin mazabun da aka soke a zaben bana.

Idan ba ku manta ba, a zaben Fubrairun bana, an dakatar da zabe a wasu akwatuna 71 a cikin Mazabu 8 na kananan hukumomin Ajeromi da Ifelodun. Yanzu dai an karasa wannan zaben kwanaki da yayi kwantai a makon jiya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel