Ba na nadamar koma wa APC - Tsohon gwamnan PDP

Ba na nadamar koma wa APC - Tsohon gwamnan PDP

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma Sanata mai wakiltar yankin IKot Ekpene da ke jihar, Sanata Godswill Akpabio, ya ce ba ya nadamar watsin da ya yi da tsohuwar jam'iyyar sa, PDP, tare da koma wa jam'iyyar APC mai mulki.

Akpabio ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kammala binne wani dan uwansa da ya mutu a garin sa na haihuwa, karamar hukumar Essien Udim.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewar har kwanan gobe ba ya nadamar yanke shawarar koma wa jam'iyyar APC.

Kazalika ya ce ba ya nadamar kawo gwamnan jihar Akwa Ibom mai ci, Udom Emmanuel, a matsayin wanda ya gaje shi bayan ya kammala wa'adin zangonsa na biyu a shekarar 2015.

A cewar sa, "ba na nadamar kawo Udom Emmanuel. Na riga na fada tun shekarar 2015 cewar, ba zan kawo wanda zai yi mulki saboda ni ba, na nemo wa jihar Akwa Ibom ne shugaba. Matukar jama'ar jihar Akwa Ibom na farinciki, babu abinda zai sa na kasa gamsuwa. Na ji dadi cewar na kawo mutumin da ya dace.

Ba na nadamar koma wa APC - Tsohon gwamnan PDP

Akpabio
Source: UGC

"Hakazalika, ko kadan ba na nadamar koma wa jam'iyyar APC. Ko a yanzu zan yanke shawara, zan zabi koma wa jam'iyyar APC a kan zama a cikin jam'iyyar PDP don na fi farincikin kasancewa dan jam'iyyar APC.

Sanatan Akpabio ya yi watsi da jita-jitar cewar zai koma jam'iyyar PDP, ya bayyana hakan da cewar sharrin makiyansa ne na siyasa.

DUBA WANNAN: Saraki ya samu sabon aiki a hukumar kasa da kasa ta IHRC

Kazalika, ya bayyaa cewar ya yi matukar farincikin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasara da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa da aka kammala.

A shekarar 2018 ne Sanata Akpabio ya canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Sai dai, canjin shekar ya jawo masa faduwa zabe a takarar neman sake koma wa kujerarsa ta sanata a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel