Hada kai da PDP: Uzor Kalu yana so a binciki manyan Jam’iyyar APC

Hada kai da PDP: Uzor Kalu yana so a binciki manyan Jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya nemi a gudanar da bincike na musamman a game da zargin da yake yi wa wasu manyan jam’iyyar APC cewa sun yi ci amanar jam’iyyar a zaben bana.

Cif Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa yana da labari cewa wasu jiga-jigan APC da ake ji da su, sun hada-kai da jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata. Uzor Kalu yayi wannan jawabi ne wajen wani babban taron APC da aka yi a Enugu Ranar Asabar.

Tsohon gwamnan yayi kira ga APC ta nada kwamiti na musamman da zai binciki wannan zargi na sa domin a gano gaskiyar maganar. Kalu ya kuma ce an fada masa cewa an samu wasu har a cikin Ministocin kasar da su ci amanar APC.

KU KARANTA: Sarakuna na neman juawa Gwamnan APC baya a zaben 2010

Uzor Kalu yake cewa babu yadda za ayi ace shugaba Buhari ya gaza samun kashi 25% na kuri’un da aka kada a jiha irin Abia. Sanatan na APC mai jiran rantsuwa yace wasu Ministocin Buhari ne su ka hada-kai da gwamnonin PDP masu mulki.

Cif Kalu ya nemi a zakulo wadannan ‘Ya ‘yan APC da aka yi amfani da su aka cuci jam’iyyar a Kudancin Najeriya, domin a hukunta su. Mutanen da su ka halarci wannan babban taro na APC sun nuna goyon bayan su a game da wannan kira.

Manyan APC irin su Sanata Chris Adighije sun yi magana wajen taron. Haka zalika, Jagoran APC a yankin na Kudu maso Gabas, Cif Ogbonnaya Onu, ya nuna cewa zaben bana ya fi na 2015 kyau.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel