Gobara ta kone muhallai 140 a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno

Gobara ta kone muhallai 140 a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ta bayyana cewa, a ranar Asabar din da ta gabata, annobar wata wutar gobara ta kone muhallai 140 a sansanin 'yan gudun hijira na Flatari da kuma Nguro da ke jihar Borno.

Gobara ta kone muhallai 140 a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno

Gobara ta kone muhallai 140 a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno
Source: UGC

Mallam Abdulkadir Ibrahim, jami'an hulda da al'umma na hukumar reshen Arewa maso Gabashin Najeriya, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri.

Wutar gobara ta kone muhallai 140 a sansanai biyu na 'yan gudun hijira da ke cikin karamar hukumar Monguno ta jihar Borno kamar yadda Mallam Abdulkadir ya bayyana a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilun 2019.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gobarar ta salwantar da muhallai 140 na kimanin mutane 371 a sansanan 'yan gudun hijirar biyu inda kawowa yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar ta.

A cewar sa, hukumar bayar da agaji tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno sun daura damarar tare da zag dantse wajen bayar da tallafi da zai kawo sauki kan radadin da 'yan gudun hijirar ke fuskanta.

KARANTA KUMA: A baya na goyi bayan gwamna Yahaya Bello amma yanzu mugayen fadawa sun dabaibaye shi - Sarkin Ibira

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnatin jihar Bauchi ta musanta zargin cewa rashin abinci ya sanya 'yan gudun hijira da ke jihar sun koma cin ganyen albasa domin tsarkake kawunan daga tsumangiyar kan hanya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel