Saraki ya samu sabon aiki a hukumar kasa da kasa ta IHRC

Saraki ya samu sabon aiki a hukumar kasa da kasa ta IHRC

An zabi shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a matsayin jakada na musamman a hukumar sa-ido a kan hakkin bil'adama ta kasa da kasa ('International Human Rights Commission' (IHRC)).

A jawabin da ya fito daga ofishin shugaban majalisar dattijan dake Abuja, an bayyanar cewar hukumar ta aiko wa da Saraki takardar bashi mukamin ta ofishin shugabanta na Najeriya da sauran kasashen Afrika, Ambasada Friday Sani. Takardar na dauke da kwanan watan ranar 16 ga watan, Maris, 2019.

Takardar ta bayyana cewar bawa Saraki mukamin ya samu sahalewar babban sakatarenta na duniya bakidaya.

Sannan ta kara da cewa, an zabi bawa Saraki mukamin ne saboda irin shugabanci mai nagarta da ya nuna a shekaru hudu da ya yi yana jagorantar majalisar dattijai.

Saraki ya samu sabon aiki a hukumar kasa da kasa ta IHRC

Saraki
Source: Depositphotos

A cikin takardar, Sani ya ce hukumar ta jinjina wa Saraki bisa halin dattako da ya nuna a mazabarsa lokacin da aka takale shi yayin zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya.

DUBA WANNAN: Hotunan dakin kwanan dalibai 10 da Dangote ya gina a jami'ar ABU Zaria

Sabon mukamin na Saraki zai bashi damar jagorantar tawagar kungiyar a taro da aiyuka daban-daban da zata ke gudanar wa a fadin duniya.

A ranar 10 ga watan Afrilu ne Saraki ya karbi sabon mukamin har ma ya nuna jin dadinsa tare da mika godiyar sa ga hukumar IHRC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel