A baya na goyi bayan gwamna Yahaya Bello amma yanzu mugayen fadawa sun dabaibaye shi - Sarkin Ibira

A baya na goyi bayan gwamna Yahaya Bello amma yanzu mugayen fadawa sun dabaibaye shi - Sarkin Ibira

Sarkin kabilar Ibira Abdul Rahman Ado Ibrahim, ya ce gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya sauka daga turbar aminci a sakamakon ruduwa da dukiya da kuma miyagun fadawa da su ka dabaibaye kujerar sa ta jagorancin al'umma.

Gwamna Yahaya Bello

Gwamna Yahaya Bello
Source: UGC

Sarki Ibrahim ya ce gwamna Bello ya rasa duk wata martaba ta aminci a idanun al'ummar jihar Kogi, kazalika samun nasarar karkato da ra'ayin su wajen goyon bayan kudirin sa na neman tazarce a kujerar sa karo na biyu abu ne mai matsananciyar wahala.

CIkin wata hirar sa yayin ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust, Sarkin gargajiyar ya hikaito yadda ya goyi bayan gwamna Bello a zaben 2015 a sakamakon kyautata masa zato da a halin yanzu ya sauka daga wannan turba ta aminci.

A cewar sa, Sarki Ibrahim ya yi babatun yadda gwamnan Bello ya yi watsi da sauraron duk wasu shawarari na masarautun jihar Kogi illa iyaka bayar da lokacin sa ga wadanda suka rike shi tamkar abin bauta.

KARANTA KUMA: Ronaldo ya ci kwallo ta 600 a fagen kungiyoyin kwallon kafa

A yayin da ya ke gudun abin da zai gurbata kyakkyawar alakar da ke tsakanin sa da gwamna Bello, Sarki Ibrahim ya yi addu'ar neman samun nasarar tazarce a gare sa duk da a fahimtar sa wannan addu'a ba za ta yiwa 'yan kabilar Ibira dadi ba.

Sai dai ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar alaka da nuna mafificin fifiko tsakanin kabilar Igala da kuma gwamna Bello fiye da yadda ta kasance a tsakanin sa da 'yan kabilar Ibira da suka kasance 'yan tsiraru a jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel