Al'amura sun daidaita a jihar Gombe bayan sanya dokar hana fita ta sa'o'i 15

Al'amura sun daidaita a jihar Gombe bayan sanya dokar hana fita ta sa'o'i 15

Al'amura sun koma dai-dai a garin Gombe da kewaye bayan an saka dokar hana fita ta sa'o'i 15 a babban birnin jihar a matsayin martani ga barazanar samun barkewar rikici a garin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar gwamnatin jihar ta saka dokar takaita zirga-zirga a garin Gombe da misalin karfe 3:00 na ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu.

Sai dai, gwamnatin jihar ta sassauta dokar bayan tuntubar hukumomi da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron jihar.

NAN ta rawaito cewar wata mota ta hallaka mambobin wata Coci su 10 tare da raunata wasu mutanen 30 yayin da suke taron ibadar bikin Ista a garin Gombe, ranar 22 ga watan Afrilu.

Al'amura sun daidaita a jihar Gombe bayan sanya dokar hana fita ta sa'o'i 15
Gwamnan jihar Gombe; Ibrahim Hassan Dankwambo
Source: UGC

An shiga halin zaman dar-dar a garin Gombe a ranar Asabar yayin da aka dauko gawarwakin wadanda suka mutu domin a binne su, lamarin da ya tilasta gwamnatin jihar saka dokar ta baci a garin don gudun barkewar sabon rikici.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta kubutar da mutane da dama daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina Ala

Mary Malum, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe, ta shaida wa NAN cewar al'amura sun koma dai-dai a garin Gombe, ta kara da cewa an aika jami'an tsaro zuwa sassan garin domin saka ido tare da dakile duk wata barazana ga zaman lafiya da kan iya taso wa.

Mallum tayi kira ga mazauna garin da su kasance masu biyayya ga doka.

NAN Ta rawaito cewar yanzu haka an bude kasuwanni, tashoshin mota da sauran wuraren harkokin jama'a da kasuwanci a garin Gombe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel