Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan Fashi da Makami 4 a jihar Neja

Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan Fashi da Makami 4 a jihar Neja

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Neja, ta samu nasarar cafke wasu kasurguman 'yan fashi da makami hudu da suka saba addabar matafiya da mazauna yankin Kanaba daura da karamar hukumar Mokwa da ke jihar.

Garba Mande, Muhammad Mande, Ahmadu Mande da kuma Muhammad Awwali da suka fito daga rifar Fulani ta Mokwa sun yi kaurin suna da cin karen ba bu babbaka na ta'addancin fashi da makami a yankin kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan Fashi da Makami 4 a jihar Neja

Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan Fashi da Makami 4 a jihar Neja
Source: UGC

Miyagun ababen hudu sun shiga hannu biyo bayan wani simame na kwanton bauna da jami'an hukumar 'yan sanda su ka gudanar a Tashar Hajiya da ke yankin Kanaba kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, masu tayar da zaune tsayen sun shiga bayan sun yiwa wata mata, Bose Adeyemi mai sayar da kayan masarufi fashi da makamin na dukiya ta kimanin N93,000 tare da wayarta ta salula.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Muhammad Abubakar, yayin bayar da tabbacin gagarumar nasara da hukumar su ta samu, ya bayar da shaidar yadda 'yan fashi da makamin su ka shiga dauke da miyagun makamai.

KARANTA KUMA: Kungiyar NGF za ta yiwa sabbin gwamnoni shirin maraba da wayar da kai

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumomin tsaro sun cafke wasu 'yan Najeriya 9 da laifin zambar dukiyar al'umma ta kimanin Dalar Amurka miliyan 3.5 a kasar Amurka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel