Da dumi dumi: An sanar da ranar sakin sakamakon jarabawar JAMB

Da dumi dumi: An sanar da ranar sakin sakamakon jarabawar JAMB

Hukumar shirya jarabawar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, JAMB ta sanar da ranar da zata fara sakin sakamakon jarabawar da dalibai masu sha’awar shiga makarantun gaba da sakandari suka zana.

Shugaban sashin watsa labaru, Dakta Fabian Benjamin ne ya sanar da haka a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace suna sa ran daga ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu zasu fara sakin sakamakon jarabawar.

KU KARANTA: Yan Najeriya 9 sun shiga hannu a kasar Amurka da laifin zamba

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu suna matakin tantance sakamakon jarabawar ne, don haka basu kammala ba, amma suna gab da kammalawa, don haka zarar sun kammala zasu sake shi daga ranar Litinin.

Haka zalika Benjamin ya tabbatar da kudurin hukumar JAMB na sake dubawa, tare da tantance sakamakon jarabawar da hukumar ta gudanar a shekarun baya, tun daga shekarar 2009, sai dai yace har sai sun saki sakamakon jarabawar 2019 zasu fara wannan aikin.

Ya kara da cewa dalilin wannan aiki na waiwaye da masu iya magana ke yi ma kirari da adon tafiya shine domin bankado duk wasu magudin jarabawa da aka yi daga shekarar 2009 zuwa 2019.

A kusan makonni biyu da suka gabata ne dalibai miliyan 1.8 suka zana jarabawar JAMB, amma ba kamar yadda hukumar ta saba yi a baya ba, inda take sakin sakamakon jarabawar cikin kwanaki biyu, a yanzu ta canza salo, kuma ta bayyana cewa da gangan tayi hakan don tabbatar da ingancin sakamakon jarabawar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel