Rundunar soji ta kubutar da mutane da dama daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina Ala

Rundunar soji ta kubutar da mutane da dama daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina Ala

Hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta ce dakarunta, dake aiki a karkashin atisayen 'Whirl Stroke' domin dakile aiyukan ta'addanci a jihohin arewa ta tsakiya, sun kubutar da wasu mutane uku da masu garkuwa da mutane suka boye a wani gida dake Gbise a karamar hukumar Katsina Ala a jihar Benuwe.

A jawabin da kakakin rundunar tsaro, Kanal Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Asabar, ya ce dakarun sojin sun kubutar da wani namiji da wasu mata biyu a wani samame da suka kai da sanyin safiyar ranar Juma'a a gidan shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ake kira da suna 'Gana'.

Ya ce an sace mutanen ne watanni biyu da suka wuce a garin Gboko sannan daga bisani masu garkuwa da su suka mayar da su garin Gbise.

Ya kara da cewa har yanzu dakarun soji na cigaba da farautar 'yan ta'addar, wadanda suka gudu bayan sun yi musayar wuta da dakarun soji.

Rundunar soji ta kubutar da mutane da dama daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina Ala

Rundunar soji
Source: Twitter

Kazalika, ya bayyana cewar dakarun sojin sun rushe gidan da masu garkuwar ke boye mutane a cikinsa.

Nwachukwu ya kara da cewa rundunar soji ta mika mutane ukun da ta kubutar ga gwamnatin jihar Benuwe domin a duba lafiyar su, sannan a mika su ga iyalinsu.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta tabbatar da kashe 'yan bindiga 4 a Zamfara

Ya ce hatta a jihar Nasarawa, dakarun rundunar atisayen 'Whirl Stroke' sun kama wani dan bindiga yayin wani samame da suka kai a mboyar 'yan ta'addar dake Alima, daf da Kadarko a Giza.

Ya ce mai laifin, wanda aka kama da wasu bindigu da aka kera a Najeriya da alburusai, yanzu haka ya na bawa rundunar sojoji muhimman bayanai a binciken da suke gudanar wa. Ya kara da cewa zasu mika shi hannun hukumomin da ya dace bayan kamma bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel