Kungiyar NGF za ta yiwa sabbin gwamnoni shirin maraba da wayar da kai

Kungiyar NGF za ta yiwa sabbin gwamnoni shirin maraba da wayar da kai

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF bisa jagorancin gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ta daura damarar kaddamar da wani shiri na yiwa sabbin zababbun gwamnonin da masu dawowa karo na biyu lale maraba da kuma wayar masu da kai.

Kungiyar NGF za ta yiwa sabbin gwamnoni shirin maraba da wayar da kai

Kungiyar NGF za ta yiwa sabbin gwamnoni shirin maraba da wayar da kai
Source: Depositphotos

NGF ta kudiri aiwatar da wannan shiri da manufa ta bayar da tallafin shawarari na rike akalar jagoranci cikin aminci da nagartar ga sabbin gwamnoni tare da wayar masu da kai a kan ababe masu nasaba ga tabbatar da ci gaban kasa.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, NGF za ta yiwa sabbin gwamnonin shimfidar tsare-tsare da fahimtar da su a kan akidu na sauke nauyin al'umma da a halin yanzu ya rataya a wuyan su da kuma mashahuran al'amurran gudanar da gwamnati.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin za ta gudanar da wannan taro na budar kai daga ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 1 ga watan Mayun 2019 inda masu ruwa da tsaki daga duk wani kwararo na kasar nan za su halarta.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya 9 sun shiga hannu a kasar Amurka da laifin zamba

Cikin wadanda za su halarci taron sun hadar da sabbin zababbun gwamnoni, tsaffin gwamnoni, kusoshin gwamnatin kasashen duniya, shugabannin cibiyoyi da manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya da makamantan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel