'Yan Najeriya 9 sun shiga hannu a kasar Amurka da laifin zamba

'Yan Najeriya 9 sun shiga hannu a kasar Amurka da laifin zamba

Hukumomin tsaro a kasar Amurka sun dakume wasu 'yan Najeriya 9 da zargin aikata laifin zambar dukiyar a kan daidaikun al'umma da kuma abokanan kasuwanci ta kimanin Dalar Amurka miliyan uku da rabi kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wannan rahoto ya fito cikin wata sanarwa daga bakin lauyan koli na gundumar kudancin birnin New York da ke kasar Amurka, Geoffrey Berman da kuma hukumar kula da bincike da leken asiri na kasar bisa jagorancin James Spero.

'Yan Najeriya 9 sun shiga hannu a kasar Amurka da laifin zamba

'Yan Najeriya 9 sun shiga hannu a kasar Amurka da laifin zamba
Source: UGC

Ababen zargin kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito sun hadar da; Oluwaseun Adelekan, Olalekan Daramola, Solomon Aburekhanlen, Gbenga Oyeneyin, Abiola Olajumoke, Temitope Omotayo, Bryan Eadie, Albert Lucas da kuma Ademola Adebogun.

Cikin rahoton da hukumomin kasar su ka bayyana a ranar Alhamis da ta gabata, ana zargin Matasan 9 da aikata laifin zamba cikin aminci ta dukiyar al'umma inda ko wane daya daga su zai fuskanci hukuncin dauri na shekaru 20 a gidan kaso.

KARANTA KUMA: Jonathan ya haramtawa tsohon hadimin sa sukar Buhari

A yayin haka cikin wani rahoton mai nasaba da wanna, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ma'aikatar tsaron Amurka ta ce tana da niyar aika karin sojoji dari uku kan rundunarta da ke aiki a kan iyakar Kudancin kasar da kasar Mexico.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel