Yan bindiga sun sace gawa a Rivers, sun nemi N1m kudin fansa

Yan bindiga sun sace gawa a Rivers, sun nemi N1m kudin fansa

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a ranar Juma’a sun sace wata gawa a Ahoada da ke karamar hukumar Ahoada ta gabas na jihar Rivers, sannan nemi a basu naira miliyan daya kudin fansa kafrin su sake ta.

Idon shaida ya bayyana cewa yan bindiga sun sace gawar wacce aka dauko daga coci domin a binne a gida, a hanyar Ahoada, bayan sun umurci direban dake tukin motar gawan da ya dakata.

Idon shaidan ya ce yan bindigan sun dauke gawar daga cikin motar sannan suka tsere da ita zuwa cikin daji yayinda suka bukaci direban ya tafi.

Yace labarin mumunan lamarin ya riski yaran marigayiyar, inda daya daga cikinsu ya ziyarci wajen da abun ya faru, amma cewa dan marigayiyar bai dawo gida da ransa ba.

Yan bindiga sun sace gawa a Rivers, sun nemi N1m kudin fansa

Yan bindiga sun sace gawa a Rivers, sun nemi N1m kudin fansa
Source: Depositphotos

Yace jim kadan bayan dan marigayiyar ya isa wajen don neman a saki gawar mahaifiyarsa, sai yan bindigan suka harbe shi sannan suka ja gawarsa zuwa cikin dajin.

Yace wani daga kauyen ya sanya baki kafin a sakarwa cocin da gawar.

KU KARANTA KUMA: Muna da kudirin takara a zaben 2023 - Ali Nuhu

Ya bayyana cewa jim kadan bayan sakin gawar sai aka fara shirin binne ta a cocin garin, sai dai aka sanar da taron cewa yan kungiyar asiri na nan zuwa kai hari inda hakan yasa kowa guduwa sannan aka bar gawar a yashe.

A lokacin da aka kira kakakin yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni yace bashi da labarin lamarin.

Yace zai kira DPO din yan sandan Ahoada don jin bayani akan lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel