Mun shiryawa Abba Yusuf da PDP a Kotu – Lauyan Gwamna Ganduje

Mun shiryawa Abba Yusuf da PDP a Kotu – Lauyan Gwamna Ganduje

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta nemi kotun da ke sauraron karar zaben 2019 a jihar Kano, da ta bayyana cewa ita ce ta lashe zaben gwamna da aka yi a maimakon Abdullahi Umar Ganduje.

Jam’iyyar tana nema kotu ta soke nasarar da gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC mai mulki ya samu a zaben na bana. PDP tana so ne a ba ‘dan takararta, Injiniya Abba K. Yusuf nasara a zaben na 2019.

Lauyoyin PDP sun fadawa kotun karar zaben cewa ‘dan takarar ta na 2019, Abba Kabiru Yusuf, ya samu kuri’un da ake nema wajen lashe zaben gwamna don haka ta nemi a tsaida sa a matsayin zababben gwamna na jihar Kano.

A karar da PDP ta maka a gaban kotun mai sauraron korafin zabe mai shafi 1685. Jam’iyyar hamayyar tana ja da soke zaben wasu yankuna a cikin karamar hukumar Nasarawa da hukumar zabe mai zaman kan-ta tayi a watan jiya.

KU KARANRA: 2019: Mu hadu a Kotu - Abba ya fadawa Ganduje

Mun shiryawa Abba Yusuf da PDP a Kotu – Lauyan Gwamna Ganduje

Lauyoyin Abba Yusuf su na nema a karbe nasara Ganduje
Source: Twitter

Wani daga cikin Lauyoyin PDP, Barista Bashir Mohammad, ya bayyanawa manema labarai cewa za a ba gwamna Abdullahi Ganduje makonni 3 ya kare kan sa a gaban kuliya, inda bayan nan Alkalan kotu za su zauna su yanke hukunci.

Haka zalika daya daga cikin masu kare gwamna Abdullahi Ganduje a gaban kotu, Barista Musa A Lawan, yace a shirye tawagarsu ta ke da ta tabbatar da gaskiyar cewa gwamna Ganduje na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben banan.

Lauyoyin Abba Kabir Yusuf sun ce PDP ta cika duk sharudan lashe zabe bayan da ta samu kaso 2 cikin 3 na mafi yawan kananan hukumomin da ake da su a jihar Kano kamar yadda sashe na 179 na kundin tsarin mulkin kasa ya bayyana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel