Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai

Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai

-Rundunar sojin Najeriya zata nemi bashin makudan kudi domin bunkasa kamfanin kera ababen hawa irin na amfaninsu

Hafsun sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ne yayi wannan batu ranar Assabar in da yake cewa rundunar sojin kasan zata nemi naira biliyan daya domin bunkasa kamfanin sojin na sarrafa ababen hawa.

Buratan ya fadi wannan maganar ne yayin wani atisaye da ya gudana a Jaji, wanda shine ya kawo karshen wani taro da hafsun sojin ya shirya na tsawon mako daya.

Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai

Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai
Source: UGC

KU KARANTA:Tinubu ba zai mulki Najeriya ba, inji shugaban Miyetti Allah

“ Muna nan muna neman yadda zamu samu kudi naira biliyan daya domin bunkasa kamfanin kera ababen hawanmu. Wannan cigaba zai yi matukar taimakama aikinmu.

“ Munada abubuwa daban-daban a karkashin rundunar tamu da suke kawo mana kudi. Ya zama dole mu nemi bashi domin karfafa wannan kamfanin namu. Manufarmu kuwa a nan itace ya kasance zamu iya kera tanka wacce ake zuwa yaki da ita, sannan kuma mu samu damar cigaba da kula da wadanda muke da su dama.” Buratai ya fadi.

Taron da akayi ya kara hada kan kowa da kowa waje daya domin ganin irin cigaban da rundunarsu ta samu cikin dan kankanin lokaci a shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel