Masoyan Sanata Melaye sun taya sa murna bayan kammala Digiri

Masoyan Sanata Melaye sun taya sa murna bayan kammala Digiri

Sanata Dino Melaye yana cikin ‘daliban da jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta yaye a karshen makon nan. Cincirondon jama’a sun fito sun taya fitaccen ‘dan majalisar murna a wannan babbar rana.

Masoyan Sanata Melaye sun taya sa murna bayan kammala Digiri

Sanatan Kogi Melaye ya kammala Digirinsa na Masters a ABU Zaria
Source: UGC

Daruruwan Masoya Sanatan na PDP, Dino Melaye, sun rika shewa su na murna a lokacin da su ka hange sa rataye da alkyabbar da wadanda su ka kammala jami’ar su ke sanyawa. An yi wannan biki ne Ranar Asabar 27 ga Afrilu.

Kamar yadda ‘dan majalisar yayi bayani da kan sa a shafukan sa na sada zumunta, Melaye ya bayyana cewa ya kammala Digirgir din sa ne a kan hulda da sha’anin kasar waje watau "International relations and diplomacy."

KU KARANTA: An yi ram da wani Gwamnan karya a Najeriya

‘Dan majalisar mai wakiltar Yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawan ya ji dadin yadda mutane su ka rika kiran sunansa, su na taya sa murna, inda yayi alkawari cewa zai yi kokari wajen ganin bai ba ‘yan Najeriya kunya a majalisa ba.

Sanatan na jam’iyyar adawa ya kuma bayyana cewa farin jinin da yake samu daga tarin jama’a, baiwa ce daga Ubangiji ba komai ba. Kafin nan dai Sanatan yayi wani Digirin a jami’ar ta Ahmadu Bello wanda aka yi ta ce-ce-ku-ce a baya.

Mun kuma kawo maku bidiyo da shafin DUA_ABUZaria su ka daura a jiya inda aka ga yadda aka tarbi ‘dan majalisar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel