Atiku Abubakar yana shirin maka Shugaban Hukumar INEC a gaban Kotu

Atiku Abubakar yana shirin maka Shugaban Hukumar INEC a gaban Kotu

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya fara tunanin maka shugaban hukumar zabe na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu a gaban kotu da laifin sabawa hukuma.

Atiku Abubakar ya soma barazanar shigar da shugaban na INEC, Mahmood Yakubu, a gaban kuliya ne a dalilin sabawa umarnin da kotu tayi na cewa a mikawa Lauyoyin sa kayan da aka yi amfani da su wajen aikin zaben da ya gabata.

Kwanakin baya ne kotun daukaka kara da ke Najeriya ta ba hukumar INEC umarni ta fito da kayan zaben 2019 domin Lauyoyin Atiku Abubakar su gabatar da wani bincike a game da shari’ar karar zaben shugaban kasa da ake yi.

Har gobe hukumar INEC ba ta cika wannan umarni da kotu ta bada tun Ranar 6 ga Watan Maris ba. Kamar yadda mu ka ji, wannan ne ya sa ‘dan takarar jam’iyyar adawar yake tunanin kai shugaban hukumar INEC kara a kotu.

KU KARANTA: Kungiyar Makiyaya sun ce Tinubu zai zai mulki Najeriya ba

Lauyoyin Atiku sun nuna cewa babu abin da za su iya a yanzu, illa su shigar da karar Farfesa Mamood Yakubu a kotu da laifin tuburewa maganar babban kotu. Lauyoyin za su nemi hukuma ta daure shugaban na INEC a gidan yari.

Mike Ozekhome SAN wanda yana cikin manyan Lauyoyin Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun yi wata kusan 2 su na aika Lauyoyi su karbo masu kayan zaben 2019 a hannun INEC, amma har yanzu hakar su a wajen INEC ba ta cin ma ruwa ba.

Lauyan ‘dan takarar na PDP bayyanawa ‘yan jarida cewa Farfesa Mahmood Yakubu ya koma yi wa dokar kasa da umarnin kotu karan-tsaye don haka dole su nemi a daure sa. Lauyan ya kuma yi magana game da hujjojin PDP da ke gaban kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel