Rundunar soji ta tabbatar da kashe 'yan bindiga 4 a Zamfara

Rundunar soji ta tabbatar da kashe 'yan bindiga 4 a Zamfara

Rundunar soji a karkashin atisayen Sharan Daji ta tabbatar da kashe 'yan bindiga hudu a jihar Zamfara.

Rundunar ta ce 'yan bindigar sun raunata dakarun soji shida a cikin wadanda suka fafata da su.

Manjo Hakeem Otiki, kwamandan rundunar soji ta 8 dake jihar Sokoto, ne ya tabbatar da hakan a wani taro da manema labarai a Gusau, wanda aka yi ranar Asabar.

Otiki ya ce lamarin ya faru ne yayin da dakarun rundunar atisayen suka fafata wani kazamin fada a dazukan karamar hukumar Shinkafi ranar Alhamis din da ta gabata.

Ya ce harin da dakarun soji ke kai wa, ta sama da kasa, da gudunmawar dakarun soji daga jamhuriyar Nijar, a kan 'yan bindigar, ya matukar rage karfinsu a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, da Katsina da wasu sassan jamhuriyar Nijar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel