Yadda wata tsohuwa ta ke yin kaca-kaca da Buhari a Bauchi

Yadda wata tsohuwa ta ke yin kaca-kaca da Buhari a Bauchi

- An ji wata Tsohuwa ta fito tana sukar Shugaba Buhari a Jihar Bauchi

- Kafin yanzu wannan Baiwar Allah tana cikin Magoya bayan Buhari

- Wannan Mata ta dade tana sukar Gwamnatin Mohammed Abubakar

Wani bidiyo da yake yawo a cikin ‘yan kwanakin nan ya shiga hannun Legit.ng Hausa, inda wata Baiwar Allah ta fito tana yin tir da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Bauchi da kuma fadin Najeriya baki daya.

Abin mamaki shi ne, wannan Dattijuwa ta taba fitowa gaban Duniya tana yabon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta ke masa addu’a Allah ya kare sa daga Makiya da Magauta, shekaru kadan da su ka wuce.

KU KARANTA: Albashi: Babu wanda ba zai tashi da kasa da N30, 000 a Najeriya

Yadda wata tsohuwa ta ke yin kaca-kaca da Buhari a Bauchi

Wata Baiwar Allah ta koma sukar Buhari bayan ta yaba masa a baya
Source: UGC

Abubakar Dadiyata, wanda wani rikakken ‘dan adawar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ne da yayi fice a kafofin sadarwa na zamani, shi ne ya fito da wannan Bidiyo kwanakin baya a kan shafin sa na Tuwita.

A wannan bidiyo wannan Mata mai shekaru 104 ta bayyana cewa a shekarun baya, tana ganin kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin yanzu. Wanna tsohuwa dai ta rika surfafawa shugaban kasar zagi.

Bisa dukkan alamu dai wannan Baiwar Allah ta fito ne daga jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin kasar. A zaben 2019 dai jam’iyyar APC mai mulki ta rasa rikon jihar Bauchi a hannun PDP.

Ga wannan bidiyo nan

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel