An kama wani mai amfani da sunan gwamna El-Rufai ya na damfarar mutane

An kama wani mai amfani da sunan gwamna El-Rufai ya na damfarar mutane

- Dubun wani saurayi ta cika da ya kware wurin amfani da sunan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya na damfarar mutane kudi a Kaduna

- Hukumar 'yan sandan jihar ce ta kama shi, inda saurayin ya amsa laifinsa kuma ya bayar da cikakken bayani akan laifin na sa

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama wani mai suna Mohammed Jamilu, wanda ya kware wurin amfani da sunan mutane, domin bata musu suna.

Wanda ake tuhumar ya kware sosai wurin amfani da sunan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya na aikata laifuka, inda ya ke tsoratar da wadanda yake cutar ta hanyoyi da dama.

An kama wani mai amfani da sunan gwamna El-Rufai ya na damfarar mutane

An kama wani mai amfani da sunan gwamna El-Rufai ya na damfarar mutane
Source: UGC

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ahmad Abdulrahman wanda ya gabatar da wanda ake zargin a hedkwatar 'yan sanda ta jihar, ya ce wanda ake tuhumar yana zuwa wurin malamai a jihar, ya na amfani da sunan gwamnan yana sanya fargaba da tsoro a zuciyarsu, domin ya damfaresu.

KU KARANTA: Kashe - kashe: An bukaci a sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna

"Mohammed Jamilu dan shekaru 30 a duniya ya kware sosai wurin amfani da suna mutane yana damfara, ya zabi ya dinga zuwa wurin manyan mutane da malamai a jihar. Ya na magana da su, inda ya ke bayyana musu cewa gwamnan Nasir El-Rufai ne ya dauke shi domin ya ga ya kawar da irinsu a jihar, ta ga wannan hanyar sai ya sanya tsoro a zuciyar mutanen, inda a karshe zai karbi kudi masu dinbin yawa ya gudu."

Kwamishinan ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma ya bayar da bayanai wanda za a iya amfani da su a kotu. Ya kara da cewa kuma sun samu nasarar kama mutane 34 wadanda ake zargin su da laifuka da yawa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel