Jagorancin majalisar dattawa: ‘Yan najeriya zasu samu kyakkyawan jagoranci daga wurina, inji Lawan

Jagorancin majalisar dattawa: ‘Yan najeriya zasu samu kyakkyawan jagoranci daga wurina, inji Lawan

-Lawan na neman goyon bayan Goje da Ndume domin ya cinma burinsa na zama shugaban majalisar dattawa

-Tsarin kamfe na gida-gida Lawan Ahmad ke amfani dashi domin kaiwa ga nasara a zaben jagorancin majalisar dattawa ta 9

Sanata Lawan Ahmad wanda shine ke kan gaba cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 9 yace zai kawo abubuwa dama idan aka zabe shi a watan Yuni.

Lawan wanda ya kasance jagoran masu rinjaye na majalisar kana kuma yana daf da cika shekaru ashirin a majalisar ta dokoki yace, yana ganin akwai kwarewa da sanin aiki tattare dashi da zai yi amfani da ita “domin ya tabbatar ‘yan Najeriya sun samu kyakkyawan jagoranci.”

Jagorancin majalisar dattawa: ‘Yan najeriya zasu samu kyakkyawan jagoranci daga wurina, inji Lawan
Jagorancin majalisar dattawa: ‘Yan najeriya zasu samu kyakkyawan jagoranci daga wurina, inji Lawan
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN:Jagorancin majalisa ta 9: PDP na shirya kaidin zaben Goje da Ekweremadu

Lawan yayi wannan furucin ne yayinda shi da tawagarsa ta kamfe suka isa shelkwtar Media Trust dake Abuja a jiya. Lawan wanda ya samu rakiyar zababbun sanatoci 11 yace komai yana tafiya yadda kamata a bangarensu kuma nasara kawai yake hangowa.

Babban editan Media Trust, Mallam Mannir Dan-Ali ne ya karbi bakuncin wannan tawaga ta Ahmad Lawan da jama’arsa tare da wasu abokan aikinsa editoci.

Daga ciki wadanda sukayi rakiya ga Lawan akwai: Francis Alimekhena (APC, Edo), Sabi Abdullahi (APC, Neja), Jibrin Barau (APC, Kano), Dayo Adeyeye (APC, Ekiti), Tolu Odebiyi (APC, Ogun), Bello Mandiya (APC, Katsina), Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti), Jibrin Isah Echocho (APC, Kogi), Olubunmi Adetunbi (APC, Ekiti) da kuma Eremienyo Wagara (APC, Bayelsa).

Lawan (APC, Yobe) yace a cikin tsarin kamfe dinsa na gida-gida zai zauna da sauran abokan takararsa wato, Muhammad Ali Ndume (APC, Borno) da kuma Danjuma Goje (APC, Gombe) domin ya gana da su tare da neman hadin kansu cikin wannan tafiya tashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel