Jagorancin majalisa ta 9: PDP na shirya kaidin zaben Goje da Ekweremadu

Jagorancin majalisa ta 9: PDP na shirya kaidin zaben Goje da Ekweremadu

-Bana akwai kallo a majalisar dattijai! PDP na neman dan takarar shugabancin majalisar da zata marawa baya

-Goje, Lawan, Ndume da Abdullahi duk suna sha'awar jagorancin majalisa ta 9

Yayinda fafutukar neman jagorancin majalisar dattijai ta 9 ke kara zafi, jam’iyar adawa ta PDP nata kokarin hada kai da daya daga cikin masu neman shugabancin majalisar.

Jam’iyar ta PDP nada niyyar marawa shugaban kwamitin kasafi na majalisar wato sanata Danjuma Goje baya a matsayin shugaban majalisar inda kuma sanata Ike Ekweremadu zai zame masa mataimaki.

Jagorancin majalisa ta 9: PDP zata goyi bayan Goje da Ekweremadu

Jagorancin majalisa ta 9: PDP zata goyi bayan Goje da Ekweremadu
Source: UGC

KARANTA WANNAN:Gbajabiamila da wasu yan majalisa 50 sun je ibada Saudiyya

Amma sai dai wasu ‘yan jam’iyar PDP na tunanin ko dai Ali Ndume da Ekweremadu ko kuma Abdullahi Adamu da Ekweremadu a matsayin yan takarar da zasu goyawa baya domin jagorancin majalisar.

Sai dai gaskiya akasarin zababbun yan majilasar dattijai na jam’iyar PDP musamman wadanda ke matukar biyayya zuwa ga shugaban majilisar Bukola Saraki sun nuna rashin amincewarsu da ko dayan Adamu da Ndume.

Saraki da wasu jiga-jigan jam’iyar PDP sunfi son Goje, wanda ya kasance babba ne a jam’iyar PDP a da kafin ya sauya sheka zuwa APC.

Wannan yinkurin da jam’iyar PDP keyi na shirin zama barazana ga dan takarar da jam’iyar APC da kuma shugaba Buhari suka aminta dashi a matsayin wanda zai kasance sabon shugaban majalisar wato sanata Lawan Ahmad.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel