Kashe - kashe: An bukaci a sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna

Kashe - kashe: An bukaci a sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna

- An bukaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Kaduna da Katsina, domin kawo karshen zubar da jini a jihohin

- Kiran ya fito daga bakin shugabannin kabilar Ijaw, da kuma matasan kabilar Igbo

Matsalar tsaro a jihar Zamfara, Kaduna da Katsina, wanda babu alamar ranar daina shi ya sanya, shugaban kabilar Ijaw, Cif Edwin Clarke da kuma matasan kabilar Igbo, bai wa gwamnatin tarayya shawara akan cewa hanya daya ce za a bi domin kawo karshen matsalar tsaron a jihohin, ita ce sanya dokar ta baci a jihohin da abin ya shafa.

Clarke da shugaban matasan kabilar Igbo, Okechukwu Isiguzoro, sun yadda cewa tunda har hanyar da gwamnati ta ke bi wurin kawo karshen zubar da jini a jihohin bai yi aiki ba, su na ganin hanya daya ce za abi domin kawo karshen matsalar, ita ce a hana mutane fita a yankunan da abin ya shafa.

Kashe - kashe: Za a sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna

Kashe - kashe: Za a sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna
Source: Facebook

Isiguzoro ya ce "Babu wata ja in ja a zancen sanya dokar ta baci a jihohin saboda an kashe rayuka masu yawan gaske a jihohin.

"Ba zai yiwu ace an cigaba da gabatar da abu daya ba kuma ana tunanin za a samu wata mafita, idan har aka sanya dokar ta baci a jihohin itace kawai hanya daya da za ta kawo karshen kashe-kashen a jihohin.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An sace wasu 'yan China a Najeriya

"Hakan ya ta ba faruwa a jihar Filato. Saboda haka idan har hanyar da ake amfani da ita a yanzu ba ta kawo wani canji ba, dole ne gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a jihohin koda na watanni uku ne.

"Idan komai ya dai-daita, kowa sai ya koma harkokinsa na yau da kullum, sannan dole ayi amfani da wannan damar a kama duk wasu da suke da hannu a zubar da jini a jihohin domin yi musu hukunci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel