Wata jiha a arewacin Najeriya ta ce ita ma ta gama shirin fara biyan sabon albashi

Wata jiha a arewacin Najeriya ta ce ita ma ta gama shirin fara biyan sabon albashi

Ana ta samun karin jihohi wadanda suke nuna cewar a shirye suke tsaf domin fara biyan sabon albashin N30,000 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu makonnin da suka gabata

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa ta gama shiri tsaf domin biyan albashin N30,000, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu domin mayar da shi doka a kasar nan.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai ta wayar salula a jiya Juma'a da daddare, kwamishin yada labarai na jihar, Ibrahim Umar Sade, ya ce, gwamnatin gwamnan jihar mai barin gado, Muhammad Abubakar, ta ce a shirye ta ke ta fara biyan sabon albashin ga ma'aikatan jihar.

Wata jiha a arewacin Najeriya ta ce ita ma ta gama shirin fara biyan sabon albashi

Wata jiha a arewacin Najeriya ta ce ita ma ta gama shirin fara biyan sabon albashi
Source: Depositphotos

Ya ce gwamnan ya bayyana cewa a shirye ya ke ya biya sabon albashin, sai dai kuma bai san ko sabuwar gwamnati da za ta karbi mulki a hannun shi za ta iya cigaba da biyan sabon albashin.

Ya kara da cewa gwamnan jihar ya na da kokarin biyan ma'aikatan jihar albashin su, ba ta re da an biyo su bashi ba, saboda yana tausaya dukkanin ma'aikatan jihar, amma matsalar ita ce ba su san halin da ma'aikatan jihar za su shiga ba, idan sabuwar gwamnati ta karbi mulki.

KU KARANTA: Babu wani ma'aikaci da zai karbi albashin kasa da N30,000 a Najeriya

Hakazalika, kungiyar kwadago ta jihar Bauchi, ta bayyana jin dadin ta ga gwamnan jihar da ya nu na cewa zai fara biyan ma'aikatan sabon albashin.

Shi ma a wata hira da ya yi da manema labarai a wayar salula, shugaban kungiyar kwadago na jihar, Comrade Hashimu Muhammad Gital, ya ce kungiyar ta na jin dadi da sabon karin albashin da gwamnatin tarayyar kasar nan ta kaddamar, saboda haka ba su ga wani dalili da zai sa ba za a fara biyan sabon albashin ba a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel