Karyane bani da niyyar barin PDP, inji Ortom

Karyane bani da niyyar barin PDP, inji Ortom

-Ortom yayi watsi da karyar da ake yi mashi cewa zai bar PDP zuwa APC

-Taya za'ayi na bar jam'iyata da tai min riga da wando, inji Ortom

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwe yayi watsi da jita-jita da ake yadawa na cewa yana shirin barin jam’iyar PDP domin komawa APC. Ortom yayi kaca-kaca da wannan magana inda ya karyata ta kai tsaye.

Otrom wanda ya sanar da manema labarai wannan batu yayinda yake ganawa da su a Makurdi yace baida wani dalilin da zai sa shi yin hakan. Da ni aka gina PDP a don haka babu abinda zai sa na barta.

Karyane bani da niyyar barin PDP, inji Ortom

Karyane bani da niyyar barin PDP, inji Ortom
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi kiristoci su dauki makamai don kare kansu a Kaduna

“ Ni nan cikakken dan jam’iyar PDP ne, ina dauke da katin shedar zama dan jam’iyar kuma a karkashinta ne nayi nasarar lashe zabe a karo na biyu. To ni kuwa mai zai kai ni komawa APC.”

Gwamnan ya sake gargadin masu yada labarin karya, da cewa wai ya baiwa gwamnan Kogi shawarar ya bar APC ya koma jam’iyar Accord inda yace ko kadan siyasar Kogi bata gabanshi.

“ Bani da masaniya akan siyasar Kogi, ni fama nakeyi da abinda kawai ya shafi jihar Binuwe wanda nake ta famar ganin na shawo kan matsalolin jihar sai dai da sauran aiki har ila yau. Me kuwa zai sani na tsoma baki cikin lamuran wata jiha daban, daga ji kasan karyace tsagwaronta.”

A fannin tsaro kuwa, ya bayyana cewa jami’an tsaro na nan tsaye bisa kafafunsu domin ganin cewa duk wanda yaso tayarda zaune tsaye an hukun tashi domin a tabbatar jihar Binuwe ta zauna lafiya gaba dayanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel