Yanzu yanzu: Buhari yayi babbar kyauta ga wata kasar yammacin Afrika

Yanzu yanzu: Buhari yayi babbar kyauta ga wata kasar yammacin Afrika

-Buhari ya baiwa kasar Giunea Bissau babbar kyauta

-Kasar Guinea Bissau ta samu kyautar makudan kudade daga wajen shugaba Buhari

Suhugaba Buhari ya bada sanarwar bada wannan gudumawa ne ta $500,000 bisa zaben da akayi a Guinea Bissau a watan da ya wuce.

Zancen da ya fito daga fadar shugaban kasar yace wannan gudunmawa dai ta biyo bayan “neman taimakon da gwamnatin Guinea Bissau tayi” wanda ya hada kayayyakin zabe 350, babur 10 da kuma mota kirar Hilux guda 5.

Yanzu yanzu: Buhari yayi babbar kyauta ga wata kasar yammacin Afrika

Yanzu yanzu: Buhari yayi babbar kyauta ga wata kasar yammacin Afrika
Source: Twitter

KU KARANTA:John Mahama, Oyegun, Otedola da Kachikwu zasu karbi lambar girma na Zik 2018

“ Duba da wannan, a matsayinsa na shugaban ECOWAS, shugaba Buhari ya baiwa ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da ya kai ziyarar gaggawa tare da babban jagoran zuwa kasar ta Guinea Bissau.

Shugaban kasar ya kara da cewa, ministan zai kai ziyara ta musamman zuwa Kotonou, babbar birnin kasar Benin domin isar da wani sako zuwa ga Shugaba Patrice Talon.

“ Ziyarar dai ta kasance ne sabili da rikici wanda ake gudun aukuwarsa ranar da za’ayi zaben yan majalisa a kasar. Zaben zai zo ne ranar 28 ga watan Afrilu, 2019.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel