Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi kiristoci su dauki makamai don kare kansu a Kaduna

Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi kiristoci su dauki makamai don kare kansu a Kaduna

Hadaddiyar kungiyar kiristocin Najeriya tayi kira ga ilahirin kiristocin dake karamar hukumar Kajuru dasu daina jiran dakarun Sojin Najeriya ko kuma Yansanda da nufin su karesu, su dauki makamai su fara kare kansu kawai.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar CAN, Joseph Hayab ne ya bayyana haka yayin da yake mika kayan tallafi da uwar kungiyar CAN ta kasa ta baiwa mutanen da rikicin kabilanci dana addini ya shafa a yankin.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya

Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi kiristoci su dauki makamai don kare kansu a Kaduna

Shugaban CAN
Source: UGC

“Ina kira ga yan uwana kiristoci damu daina jiran gwamnati ta kare yankunanmu, muma zamu iya kare kanmu, idan har zaka iya gina gidan kanka, amma kuma kana jiran Sojoji ko Yansanda su kareka toh kana da matsala.

“Babu wata doka a Najeriya data hanaka kare kanka, ita kawai doka ta hanaka cutar da wani ne, don haka bamuce ku cutar da wani ba, amma ku kare kanku, kare gidanka nada goyon baya a kundin dokokin kasa.” Inji shi.

Sai dai a wani mataki na mi’ara koma baya kuma, Faston yayi kira ga gwamnati data kare al’ummomin da makiyaya suka lahantasu domin su samu damar komawa gona duba da cewa damuna na karatowa, inda ya bada tabbacin CAN zata basu abincin ci, kuma zata basu kayan gini don sake gidajensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel