Hukumar NYSC ta samu sabon shugaba a wani garambawul da Buratai ya gudanar

Hukumar NYSC ta samu sabon shugaba a wani garambawul da Buratai ya gudanar

Rundunar mayakan Sojan kasa ta sanar da sabbin nade naden mukamai ga wasu manyan hafsoshin sojan kasa a wani aikin garambawul da gyaran fuska da babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai yake gudanar a rundunar.

Kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana wadannan sabbin nade nade, inda yace Buratai ya amince da dauke da Manjo Janar Sule Kazaure daga hukumar NYSC dake kula yan bautan kasa, inda ya sauya masa wajen aiki zuwa cibiyar bayanai ta rundunar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ta ruwaito da wannan ne Buratai ya nada Birgediya Janar S Ibrahim a matsayin sabon shugaban hukumar NYSC, bayan ya daukeshi daga jami’ar rundunar sojan kasa dake Biu, jahar Borno.

Haka zalika sanarwar ta sanar da dauke Birgediya Janar CA Bossman daga cibiyar littafai ta rundunar zuwa mukamin daraktan sashin kula da makarantun sakadandarin Sojoji dake duk fadin Najeriya, yayin da Birgediya Janar E Angaye ya zama sabon darakta mai kula da tsofaffin Sojoji.

Bugu da kari an dauke Birgediya BA Tsoho daga shelkwatar rundunar Sojan kasa zuwa cibiyar koyar da harsuna na rundunar Sojan kasa a matsayin babban kwamanda, yayin da Birgediya Janar AA Goni ya maye gurbin daya bari a shelkwata.

Sanarwar bata tsaya nan ba sai da sanar da dauke Birgediya Janar FC Onyeari daga sashin sufuri a shelkwatar rundunar Sojan kasa zuwa matsayin mukaddashin darakta mai kula da ciye ciye da tande tande.

Daga karshe babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da nada Birgediya Janar SS Ibrahim a matsayin sabon jami’i mai kula da daukan dalibai da daukan ma’aikata na jami’ar sojan kasa dake Biu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel