An kashe mutum 3 sakamakon barkewar rikici a wani bangaren jihar Kaduna

An kashe mutum 3 sakamakon barkewar rikici a wani bangaren jihar Kaduna

-An sanya dokar ta baci tsawon awa 24 a Kasuwan Magani

-Rikici ya sake barkewa a karamar hukumar Kajuru dake Kaduna

Mutane uku sun mutu sakamakon barkewar riciki a garin Kasuwan Magani dake jihar Kaduna. Kawo yanzu dai jami’an tsaro sun gaza cafke wadanda sukayi wannan ta’asa.

A nata yinkurin kawar da rikici a yankin, gwamnatin Kaduna ta saka dokar ta baci ta awa 24 a fadin karamar hukumar Kajuru.

An kashe mutum 3 sakamakon barkewar rikici a wani bangaren jihar Kaduna

An kashe mutum 3 sakamakon barkewar rikici a wani bangaren jihar Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA:2019: Su wanene za su zama Ministocin Buhari daga irin su Kano da Katsina

Yayinda yake zantawa da wakilinmu, Samuel Aruwan yace saka wannan dokar tabaci ya zama dolene domin kare yaduwar wannan rikici zuwa kauyukan dake makwabtaka da Kasuwar magani.

Ya kuma kara do rokon jama’a da su ba gwamnati da kuma jami’an tsaro goyon baya domin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin nasu dama jihar ta Kaduna baki daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel