Gbajabiamila da wasu yan majalisa 50 sun je ibada Saudiyya

Gbajabiamila da wasu yan majalisa 50 sun je ibada Saudiyya

-Wata sabuwa, 'yan majalisar wakilai sun kai siyasa kasa mai tsarki

-Sheikh Dahiru Bauchi ya goyin bayan Femi na ya kasance kakakin majalisa ta tara

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai kuma dan takarar zama kakakin majalisa ta 9, Femi Gbajabiamila ya kai kamfe dinshi zuwa kasar Saudiya inda ya tafi domin yin umara.

Sama da zababbun ‘yan majalisa 50 ke tare dashi a can. Inda kuma wannan sanannen malamin addinin musulunci a arewacin Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya nuna amincewarsa da Femi ya kasance kakakin majalisa ta 9.

Wani babban hadimin Gbajabiamila, Olanrewaju Smart ya fadi wata magana a daren Laraba inda yake cewa maigidansa na samun goyon baya daga ciki da wajen majalisar tarayya.

Gbajabiamila da wasu yan majalisa 50 sun kai siyasa kasar Saudiya

Gbajabiamila da wasu yan majalisa 50 sun kai siyasa kasar Saudiya
Source: UGC

KU KARANTA:Malaman sakandare sunyi zanga-zanga saboda rashin albashin tsawon wata 7 a jihar Ekiti

Kamar yadda ya fadi: “Sanannen malamin muslunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a yau (Laraba) ya nuna goyon bayansa ga Gbajabiamila inda ya hada mashi da addu’ar samun nasara domin ya kasance kakakin majalisa ta 9.

“ Goyon bayan da akayi ya zo ne harabar masallacin harami dake Saudiya, wannan kuma itace nuna goyon baya na karshe da akayiwa Gbajabiamila daga wajen majalisar tarayya.

“ Shugaban masu rinjayen dai ya tafi kasar Saudiya ne domin yin umara, inda zai dawo bada jimawa domin ya cigaba da kamfe dinsa har zuwa 10 ga watan Yuni inda za’a ranstsar da sabbin shugabannin majalisar tarayya.

“ Sama da mutane 50 ne daga cikin zababbun ‘yan majalisar dake wakiltar jihohi 36 na fadin kasar nan ke tare dashi a Saudiya.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel