Kwararrun likitoci daga kasar waje sun shigo Najeriya don duba Zakzaky (Hoto)

Kwararrun likitoci daga kasar waje sun shigo Najeriya don duba Zakzaky (Hoto)

A iya cewa wannan shine karon farko da gwamnatin tarayya ta amince ma wasu likitocin kasar waje samun ganawa da shugaban yan shia, Ibrahim Zakzaky domin duba lafiyarsa tun bayan kamashi a shekarar 2015.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito likitocin sun samu damar ganawa da Zakzaky ne bayan samun umarni daga Alkalin wata babbar kotu dake jahar Kaduna, wanda ke sauraron karar da gwamnatin jahar Kaduna ta shigar da Zakzaky.

KU KARANTA: Zababben gwamnan Borno ya dauki alkawarin cigaba da ayyukan alherin Kashim

Kwararrun likitoci daga kasar waje sun shigo Najeriya don duba Zakzaky (Hoto)

Likitoicn, Zakzaky da matarsa
Source: Facebook

Duba da halin rashin lafiya da shugaban yan shi’an yake ciki ne yasa Alkalin ya umarci hukumar tsaron sirri wanda ke rike da Zakzaky da matarsa Zeenatu, dasu gaggauta gayyato masa likitocin da yake so don su duba lafiyarsa dana matar tasa.

Tunda fari dai lauyan Zakzaky, Femi Falana ne ya nemi wannan bukata daga Alkalin kotun, bayan ya bata bayanin cewa har yanzu Zakzaky da matarsa suna fama da matsanancin ciwo sakamakon raunuka da suka samu daga harbin bindiga da Sojoji suka yi musu a yayin da suke kokarin kamasu a shekarar 2015.

Haka kuwa aka yi, hukumar DSS ta bi umarnin kotu, inda ta baiwa likitocin damar ganawa da Zakzaky da matarsa a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu a inda suke tsare dasu, sai dai basu bayyana ma manema labaru wata magana game da abin dake damun Malamin ba.

Idan za’a tuna a can kwanakin baya da dadewa an yi ta yada jita jitan Malamin ya mutu a hannun DSS, inda daga bisani hukumar DSS ta karyata batun, har ma ta bayyanshi ga manema labaru, kuma ya bayyana musu cewa yana samun kulawa, amma baya jin dadi sosai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel