Ma'aikatan jihar Kogi sun koma bara saboda ba a biyansu albashi

Ma'aikatan jihar Kogi sun koma bara saboda ba a biyansu albashi

- Rahotanni sun nuna cewa wahala da rashin kudi ya tilasta ma'aikatan gwamnati na jihar Kogi komawa bara saboda matsalar rashin albashi

- Kungiyar kwadago ta jihar ta ce akwai ma'aikatan da suke bin gwamnatin jihar albashi kusan na watanni talatin wanda har yanzu ba a biya su ba

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kungiyar kwadago ta kasa (NLC) yankin jihar Kogi, ta ce yanzu ma'aikatan jihar Kogi sun koma bara a titi saboda rashin biyansu albashi da gwamnatin jihar ta yi.

Shugaban kungiyar na jihar, Onuh Edoka, yayin da ya ke jawabi a wani taro da ya halarta a garin Lokoja, babban birnin jihar, ya ce ma'aikata da yawa sun gagara ciyar da iyalansu, saboda suna bin gwamnati bashin kusan watanni 30.

Ma'aikatan jihar Kogi sun koma bara saboda ba a biyansu albashi
Ma'aikatan jihar Kogi sun koma bara saboda ba a biyansu albashi
Source: Facebook

Ya ce abinda ya fi kowanne muni ma shine yadda gwamnati ta ke biyan ma'aikatan karamar hukuma albashi kadan kadan na tsawon shekaru.

Edoka, ya bukaci gwamnatin jihar da ta canja wannan halayyar ta hana ma'aikata albashi, bayan suna aiki kai da kafa wurin ganin sun biya gwamnati hakkinta.

KU KARANTA: Babu wani ma'aikaci da zai karbi albashin kasa da N30,000 a Najeriya

Bayan haka Edoka, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta bada sauran kudin da ake binta N30.8b don bai wa gwamnatin jihar damar ma'aikatan albashin da suke binta na tsawon watanni.

Gwamnan jihar, Alhaji Yahaya Bello, ya yi alkawarin biyan ma'aikatan jihar albashin su, da zarar gwamnatin tarayya ta bayar da bashin da jihar ta ke binta.

Bello, wanda ya yi magana ta bakin shugaban ma'aikatan sa, Edward Onoja, ya ce ya yi alkawarin cigaba da tabbatar da jin dadin ma'aikatan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel