Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya

Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana babbar hanya mafi inganci wajen yaki da ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, inda yace samar da ingantaccen ilimi shine kadai hanyar kawar da Boko Haram daga ban kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne garin Maiduguri yayin ziyarar kwana daya daya kai jahar Borno a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, inda ya kaddamar da manya manyan ayyukan more rayuwa da gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima ya yi.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana shige-da-fice a Kaduna na sa’o’i 24

Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya

Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya
Source: Facebook

“Wannan shine dabarar kawar da ta’addancin Boko Haram, ilimi na taka rawa sosai wajen samar da gogayya tsakanin mutane tare da inganta rayuwarsu.” Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka zalika Buhari ya tabbatar ma jama’an jahar Borno cewa yana aiki kan jiki kan karfi wajen ganin ya ceto rayukan yan matan Chibok da yan matan Dapchi da kungiyar Boko ta sace a shekarun baya.

“Ba zamu hakura ba, a matsayina na shugaban kasa, dan Najeriya kuma Uba, nima ina jin zafin da iyayen yaran nan suke ji na rashin yayansu da aka sace, zamu yi duk mai yiwuwa don ganin mun sadasu da iyalansu.” Inji shi.

Haka zalika Buhari ya jinjina ma gwamnatin jahar Borno bisa namijin kokarin da tayi wajen sake farfado da jahar ta hanyar gina gidaje don sake tsugunar da jama’an da rikicin Boko Haram ya shafa, da kuma gina makarantu don ilimantar da yaransu.

A jawabinsa, Gwamna Shettima ya yaba da goyon baya da gudunmuwar da Buhari ya baiwa jahar Borno, inda ya shaida masa cewa jahar na fama da talauci, tabarbarewar ilimi da matsalolin muhalli tun kafin barkewar rikicin Boko Haram, don haka ya roki Buhari ya mayar da manyan makarantun jahar zuwa na gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel